
Rahotanni sun bayyana cewa, akwai yiyuwar farashin man fetur zai sake sauka saboda farashin danyen man fetur din wanda daga cikinsa ake fitar da man fetur din yana ci gaba da sauka.
Hakan zai kuma kara tabbata ne muddin aka ci gaba da samun karuwar karfin kudin Naira.
Farashin danyen mai ya fadi ne saboda sanarwar da kungiyar OPEC ta fitar cewa zata kara yawan man fetur din da take hakowa