Lakurawa sun yi ajalin ‘yan sa-kai 13 a Kebbi
Lamarin ya faru a karamar hukumar Augie a yankin Morai bayan da ‘yan sa-kan suka yi kokarin hana Lakurawa daukar dabbobin mutanen yankin.
Gwamna Nasir Idris na jihar ta Kebbi a ranar Lahadi ta cikin sakon ta‘aziyya a shafin Facebook, gwamnan ya yi allawadai da harin wanda ya ce ya girgiza shi.

Da sayin safiyar yau litinin maigirma Gwamna jihar kebbi Comrd Dr Nasir idris kauran malam Abdullahin Gwandu Tare Da maigirma shugaban hukumar bada Agajin gagawa Ta jahar kebbi Barrister Hon Muhammad bello yakubu Rilisco sun sami isah karamar hukumar mulki Ta Augie wurin Gaisuwar Rasuwa mutanen Da lakurawa suka kashe jiya Allah ya jikansu Da Rahama yasa su Aljana fidausi