
Lamari tsakanin Sanata Godswill Akpabio wanda shine kakakin majalisar dattijai da sanata Natasha Akpoti dake zarginsa da neman yin lalata da ita ya kara kazancewa.
Mijin Natasha, High Chief Emmanuel Uduaghan ya bayyana cewa, yasan da maganar neman matarsa da sanata Godswill Akpabio ke yi.
Yace asalima Sanata Godswill Akpabio abokinsa ne dan haka a matsayinsa na basarake kuma suna da alaka me karfi tsakaninsa da Sanata Godswill Akpabio bai nemeshi da fada ba, ya sameshi suka warware matsalar tsakaninsu inda ya mai alkawarin ya daina neman matarsa.
Saidai, High Chief Emmanuel Uduaghan yace matarsa ta ci gaba da kawo mai korafin cewa, Sanata Godswill Akpabio ya ci gaba da neman yin lalata da ita.
Dan hakane High Chief Emmanuel Uduaghan yake neman cewa a girmama matarsa wajan binciken da ake yi, yace ya yarda da matarsa kuma bata cin amanarsa.
A bangare guda kuma, a ci gaba da fallasa da Sanata Natasha kewa Sanata Godswill Akpabio, tace yayi kokarin baiwa mijinta guraben aiki da yace ya kawo duk wanda yake so za’a daukeshi aiki dan ya rufe masa baki.
Sanata Natasha tace a dambarwarsu ta farko a bainar jama’a inda Sanata Akpabio ya ce mata ta daina magana kamar suna gidan rawa a yayin da ta tashi take magana a majalisar tarayya.
Tace bayan ta koma gida a daren ranar da suka yi cece-kuce, Sanata Godswill Akpabio ya kirata inda ya bata hakuri sannan yace da safe idan sun je majalisa zai fada a gaban kowa cewa ta yi hakuri, inda ya nemi cewa dan Allah ta tashi ta ce ta hakura.
Yace suna wayar mijinta ya amsa inda ya gayawa mijinta cewa idan yana da masu neman aiki ya kawo akwai guraben daukar aiki.
Tace anan ne ta karbe wayar daga hannub mijinta saboda tana jin abinda yake gayawa mijin nata inda tace nan ta yi mai tatas saboda yaya zai tozartata a idon Duniya amma ya dawo yana neman kulle mata baki ta hanyar mijinta?
Sanata Natasha Akpoti ta bayyana hakane a yayin da aka gayyaceta wani gidan talabijin dan bayyana abinda ya faru tsakaninta da sanata Godswill Akpabio.