Fadar Sarkin Musulmi a Najeriya ta ayyana yau Laraba 1 ga watan Janairu a matsayin 1 ga watan Rajab na shekarar Hijira ta 1446.
Wata sanarwa da Wazirin Sokoto Farfesa Sambo Wali ya fitar a daren da ya gabata ta ce Sarkin Musulmi Sa’ad Abubukar III ne ya bayyana hakan bayan ganin jaririn watan.
Rajab shi ne wata na bakwai a kalandar Musulunci, wanda Hausawa ke yi wa laƙabi da watan Azumin Tsofaffi.