
Kungiyar likitoci ta gargadi masu shafa ma kara hasken fata da cewa suna cikin hadarin kamuwa da munanan cutuka irin su ciwom suga, Kansa, da ciwon Koda.
Dan haka kungiyar Likitocin me suna NAD ta bayyana cewa zai fi kyau mutane su rika barin fatarsu yanda take dan hakan zai fi basu kwanciyar hankali.
Shugaban Kungiyar Likitocin, Prof. Dasetima Altraide ne ya bayyana hakan a wajan wani taron karawa juna Sani da ya faru a Legas.
Yace yawanci sinadaran da aka hada man dasu ne ke jefa mutanen dake amfani da mayukan hasken fatar cikin matsalar rashin lafiya.