Babban maganin dena zina shine tsoron Allah.
Mutum ya tuna da irin tarin azabar da Allah ya tanadarwa mazinata ya daina.
Sannan mutum ya tuna da gargadin da Allah yawa mutane na cewa kada su kusanci zina.
Allah madaukakin sarki ya fada mana a Qur’ani cewa,’ Kada ku kusanci Zina, Alfashace kuma hanya ce ta shedan’ Qur’an 17:32.
Hakanan an samu bayanai na azabobi kala-kala da Allah kewa mazinata:
Daya daga ciki shine mafarkin da Annabi(Sallallahu Alaihi Wasallam) yayi inda aka nuna masa wani daki kamar inda ake gasa biredi da ake hura wuta a cikinsa da mutane mata da maza tsirara a ciki, yayin da wutar ta huru sai su yi saman dakin suna kururuwa, yayin da ta yi kasa, sai su koma, haka ake ta musu azaba. Da ya tambayi laifinsu, sai aka ce masa, mazinata ne.
Hakanan Sahihin Hadisi na Abu Dawood Allah ya kara yadda dashi ya tabbatar cewa a yayin da mutum ke zina, imaninshi na fita data jikinshi yayi sama kamar girgije ko hadari har sai ya kammala zinar sannan ya dawo jikinsa, kamar yanda Annabi (Sallallahu Alaihi Was Sallam) ya bayyana.
To ka yi tunanin idan mutum ya mutu yana tsaka da aikata zina ya kenan?
Saboda girman laifin zina, ana jefe mace da namijin da suka taba aure idan suka aikatata har sai sun mutu.
Ya tabbata a hadisi sahihi cewa, daya daga cikin mutanen da Allah ba zai kallah ba ranar tashin qiyama, akwai tsoho mazinaci.
Hakanan Ibn Khuzaymah da Ibn Hibbaan sun ruwaito Abu Umaamah yace, Manzon Allah (Sallallahu Alaihi wasallam) yace wata rana yana bacci aka daukeshi Inda aka nuna mai azabobi iri-iri da akewa mutanen wuta, daya daga ciki sune wasu mutane da jikinsu a kumbure take kuma yana fitar da ruwa me wari sosai, da ya tambayi laifinsu sai aka ce masa mazinata ne.
Dan haka babban maganin barin zina shine tsoron Allah da tunanin irin azabobin da ya tanadarwa mazinata.
Sauran Hanyiyin Daina Zina
Mun kawo tsoron Allah a farko saboda wasu da aurensu suke aikata zinar.
Hanya ta gaba shine mutum yayi aure ko kuma idan yana da auren in yana da hali ya kara dan ya rika biyan bukatarsa ta hanlastacciyar hanya.
Sauran hanyoyin daina zina sun hada da yin azumi, kamar yanda Annabi (Sallallahu Alaihi Wasallam) ya baiwa matasa shawarar yin aure, Wanda kuma basu da hali su yi azumi Dan yana dakushe kaifin sha’awa.
Mutum zai iya yin azumin litinin da Alhamis, ko kuma yau yayi gobe ya huta, daidai iyawar mutum.
Mutum ya guji shan lemun tsami ko kanwa wai dan rage sha’awa, wadannan sinadaraine Wanda idan suka yi yawa a jikin mutum zasu iya cutar da mutum azumi ne babbar hanyar dakushe sha’awa.
Idan akwai abokai dake zuga mutum yana aikata zinar, to yayi kokarin rabuwa dasu ko kuma ya musu nasiha duka su taru su tuba.
Idan gari ko unguwar da yake zaunene ke sanyawa yana aikata zinar, shima sai ya bar gurin.
Idan mutum bai da Sana’a ko aikin yi, yayi kokari ya nema dan zaman banza na kawo tunane-tunane marasa amfani.
Mutum ya daina kallon fina-finan batsa da kallon matan da ba nashi ba ko Matan da ba muharramanshi ba, ya daina hira da matan da ba nashi ba yana jin dadin kalamansu.
Magana ta karshe shine, kin ko ka dauki mataki me kyau na farko na hanyar shiriya watau kyamar laifin da kike ko make aikatawa, dama matakan tuba shine nadama akan abinda ake aikatawa da kuma niyyar ba za’a koma aikata laifin ba.
Mutum kuma rika jin zafin abinda ya aikata da tunanin ya zai kare da Allah.
Allah ya tsaremu baki daya.