Sunday, January 26
Shadow

Maiɗakin Tinubu ta musanta cewa za ta jagoranci yi wa ƙasa addu’a

Matar shugaban Najeriya, Sanata Oluremi Tinubu, ta musanta rahoton da ke cewa za ta jagoranci taron yi wa ƙasa addu’a saboda tarin matsalolin da Najeriya ke fama da su.

A ranar Lahadi da ta wuce wani rahoto da aka fitar ya bayyana cewa matar shugaban ƙasar tare da mai bai wa shugaban shawara kan harkokin tsaro na ƙasa, Nuhu Ribadu za su jagoranci taron kwana bakwai na yi wa ƙasar addu’a kan halin da take ciki.

Rahoton ya bayyana cewa Darakta Janar na Taron yi wa kasa Addu’a, Segun Afolorunikan, shi ne ya yi sanarwar a wani taron manema labarai a Abuja, ranar Lahadi da ta wuce.

Karanta Wannan  Kalli Bidiyo: Wata Sabuwa ana rade-radin wani babban dan siyasar Najeriya dan luwadi ne, ya mayar da martani

A waccan sanarwar Afolorunikan ya ce taron wanda aka tsara tare da jagororin addinin Kirista da Musulmi, zai buƙaci Allah Ya shiga al’amarin ƙasar kan matsalolin zamantakewa da tattalin arziki da kuma tsaro.

Sai dai a wata sanarwa da mai magana da yawun maiɗakin shugaban ƙasar, Busola Kukoyi, ta fitar a yau Asabar, ta ce, maganar ba ta da tushe balle makama.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *