Saturday, March 22
Shadow

Majalisar Dattawa ta amince da ayyana dokar ta-ɓaci a jihar Rivers

Majalsiar Dattawa ta amince da dokar ta-ɓaci da shugaban Najeriya, Bola Tinubu ya ayyana a kan jihar Rivers a ranar Talata.

Majalisar dai ta shiga tattaunawar sirri bayan da shugaban majalisar Godswill Akpabio ya karantar wasiƙar a zauren.

Shugaban masu rinjaye na majalisar, Sanata Opeyemi Bamidele ne ya karanta buƙatar shiga tattaunawar ta sirri bisa dogaro da doka mai 135 ta kundin majalisar.

Shugaban marasa rinjaye, Sanata Abba Moro ne ya amince da shiga ganawar sirrin.

Da ma dai majalisar wakilai ta amince da wannan dokar ta ta-ɓaci a ranar Alhamis.

Karanta Wannan  Shugaba Tinubu ya kaddamar da titin Legas zuwa Ibadan da aka kammala

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *