
Majalisar dattawan Najeriya ta ɗage tattaunawa kan ƙudirin farko da za su tafka muhawara a zamansu na yau game da amincewa da dokar ta-ɓaci a jihar Rivers ba tare da bayar da dalilin jinkirin ba.
A yanzu majalisar za ta zauna kan wannan batu da ƙarfe uku na rana.
An yi tsammanin za a tafka muhawara kan ƙudirin wanda shugaban masu rinjaye na majalisar dattawa, Opeyemi Bamidele ya gabatar, da safiya sai dai ƴanmajalisar sun ɗage tattaunawar.
Ƙudirin dai ya bayyana damuwa game da ruruwar tashin hankali da ya jefa jihar Rivers cikin garari tare da haifar da koma-baya a tafiyar da al’amuran gwamnati.
Gidan Talabijin na Channels ya ruwaito cewa kafin dokar ta-ɓacin ta soma aiki, dole ne sai ƙudirin ya samu goyon bayan kashi ɗaya bisa uku na ƴanmajalisar – 73 cikin sanatoci 109.
A yanzu dai hankalin ƴan Najeriya ya karkata kan majalisar dokokin Najeriya domin jin yadda za ta kaya game da dokar ta-ɓacin da Shugaba Tinubu ya ƙaƙaba a Rivers ta tsawon wata shida.