Thursday, May 22
Shadow

Majalisar Dattawan Najeriya ta kafa kwamitin kula da mulkin jihar Ribas

Majalisar Dattawan Najeriya ta kafa kwamiti mai mambobi 18 domin sanya idanu kan yadda gwamnan riƙo na jihar Ribas Vice Admiral Ibok Ete Ibas mai ritaya ke tafi da aikinsa.

Majalisar ta ce ta ɗauki matakin ne a wani yuƙuri na ƙarfafa shugabanci na gari ba tare da rufa-rufa ba a jihar da ke kudu maso kudancin Najeriya.

Shugaban Majalsiar Dattawa Godswill Akpabio ya sanar yayin zaman majalisar na yau Talata cewa kafa kwamitin na da matuƙar mahimmancin wajen sa ido kan abubuwan da ke faruwa a jihar.

Shugaban masu rinjaye Opeyemi Bamidele ne shugaban kwamatin, mambobin kuma sun haɗa da Adamu Aliero, da Osita Izunaso, da Osita Ngwu, da Kaka Shehu, da Aminu Abass, da Tokunbo Abiru, Adeniyi Adebire.

Karanta Wannan  Kalli Bidiyo yanda Matasa 'yan Izala suka rude suna ta tambayar ta yaya ake shiga Darika bayan da suka ga wata Budurwa na juya mazaunanta a wajan da Hallara ta yi girgiza

A watan Maris ne Shugaban Ƙasa Bola Tinubu ya ayyana dokar ta-ɓaci a Ribas sakamakon abin da ya kira “karyewar doka da oda” wanda ya auku sanadiyyar rikicin siyasa tsakanin Gwamna Fubara na PDP mai adawa da tsohon Gwamna WIke mai ƙawance da APC mai mulki.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *