Friday, December 26
Shadow

Majalisar Dinkin Duniya tace za’a yi yunwa me tsanani a Arewacin Najeriya

Majalisar Dinkin Duniya ta fitar da rahoto kan kasashen dake fuakantar ibtila’in yunwa su 13.

Rahoton yace kasashen Gaza, Sudan, South Sudan, Haiti,da Mali na fuskantar yunwa nan take idan ba an kai musu dauki ba.

Rahoton yace rashin tsaro, Rashin tabbas na tattalin arziki da canjij yanayi ne ya kawo lamarin yunwar.

Rahotanni ya bayyana matsalar tsaro a Arewacin Najeriya wanda yace zai iya kara kazancewa.

Rahoton yace matsalar tsaron Arewar zai kara jefa mutane cikin yunwa saboda za’a raba mutane da yawa da muhallinsu.

Karanta Wannan  Mutane Miliyan 1.9 ne suka nemi aikin Fire Service, Immigration, da Civil Defence da aka bude kwanannan, yayin da mutane dubu 30 ne kadai za'a dauka, Kalli Yawan mutanen da suka nema daga kowace jiha

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *