
Rahotanni sun bayyana cewa, Majalisar jihar Kano ta goyi bayan Gwamnan jihar, Abba Kabir Yusuf ya koma jam’iyyar APC.
Shugaban masu rinjaye na majalisar, Lawan Hussaini ne ya bayyana hakan a ganawa da manema labarai inda yace ba zai yiyu su ci gaba da zama a jam’iyyar NNPP ba saboda rikicin dake cikin jam’iyyar yayi yawa.
Yace ba zasu yadda abinda ya faru a jihar Zamfara ya faru dasu ba.
Ya kara da cewa suna goyon bayan Hadda Kwankwaso su canja jam’iyya saboda rikicin jam’iyya ya mamaye jam’iyyar NNPP.