
An yi sa insa tsakanin Majalisar Koli ta Addinin Musulunci NSCIA da kungiyar Kiristoci ta PFN a Najeriya.
Inda majalisar koli ta Addinin Musulunci a Najeriya take cewa babu maganar Khisan kiyashi da akewa mutane a Najeriya.
Ta zargi wasu bata gari a Najeriya bisa hadin gwiwar wasu ‘yan kasashen yamma da shirin amfani da sunan ana Mhuzghunawa Kiristoci su lalata Najeriya.
Sakataren kungiyar NSCIA, Prof. Is-haq Oloyede a yayin da yake ganawa da manema labarai a Abuja ranar Lahadi ne ya bayyana hakan.
Yace rikicin Najeriya ba na addini bane, Canjin yanayi, da Talauci, da Aikata Miyagun Laifuka, da rashin shugabanci na garine ya jawo abinda ke faruwa a Najeriya.
Saidai a nasa bangaren, shugaban kungiyar Kiristoci ta PFN,Bishop Wale Oke ya bayyana cewa, maganar gaskiya anawa Kiristoci Khisan Kyiyashi a kasarnan.
Yace kuma an usa kaisu Bango.