
Majalisar tarayya za ta yi bincike kan matsalolin da aka samu a JAMB ta bana
Majalisar Wakilai ta yanke shawarar gudanar da bincike kan kuskuren fasaha da ya shafi sakamakon Jarrabawar UTME na shekarar 2025.
Majalisar ta amince da wannan kuduri ne a zaman ta na ranar Alhamis, bayan ta amince da kudurin gaggawa mai muhimmancin jama’a da dan majalisa daga jihar Osun, Adewale Adebayo, ya gabatar.