
Majalisar tarayyar Najeriya dake Abuja ta dage zaman da ya kamata ta yi dan Alhinin tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari da ya rasu.
Wakilin majalisar, Kamoru Ogunlana ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar.
Yace ba zasu sake yin wani zama ba sai ranar Talata, 22 July, 2025.
Yace shugaban majalisar ne ya bashi umarnin sanar da hakan.
Ya kuma mika ta’aziyyar su ga iyalan shugaban inda ya jinjina masa wajan kokarin da yayi na hadin kan Najeriya.