Wednesday, March 19
Shadow

Majalisar wakilan Najeriya na son a ƙwace ikon yi wa jam’iyyu rajista daga wurin INEC

Majalisar Wakilan Najeriya ta gabatar da wani ƙudirin da zai ƙwace wa hukumar zaɓen ƙasar ikonta na yi wa jam’iyyun siyasar ƙasar rajista da kula da ƙa’idojin jam’iyyun.

ƙudurin – wanda kakakin majalisar wakilan ƙasar Hon.Tajudeen Abbas tare da haɗin gwiwar Hon Marcus onobun daga jihar Edo suka gabatar – ya buƙaci a samar da wata hukuma mai zaman kanta da za ta kula da batun yi wa jam’iyyu rajista da kula da ƙa’idojinsu da ɗaukar nauyin jam’iyyun.

Tuni dai ƙudirin ya wuce karatu na biyu a zauren majalisar.

Haka kuma ƙudirin ya buƙaci da kafa kotu ta musamman don sauraron ƙorafe-ƙorafen jam’iyyu domin magance rigingimu tsakanin mambobin jam’iyyu.

Karanta Wannan  Ba'a kwace min Fili a Abuja ba>>Inji Tsohon Shugaban kasa, Muhammadu Buhari

Yayin da yake gabatar da ƙudirin, Hon. Onobun ya ce matakin ya zama wajibi, la’akari da yadda ake yawan samun rigingimun tsakanin jam’iyyu da mambobinsu

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *