Thursday, May 22
Shadow

Makaranta a Najeriya ta kori ɗalibar da ta fallawa malami mari kan ya hanata TikTok

Hukumomin Jami’ar Nnamdi Azikiwe da ke, Awka a jihar Anambra ta kori ɗalibar nan, Goddy-Mbakwe Chimamaka Precious, saboda cakuma tare da cin kwalar wani malamin jami’ar.

A cikin wani bidiyo da ya karaɗe shafukan sada zumunta an ga ɗalibar ta far wa malamin jami’ar, Dr Chukwudi Okoye, bayan ya ratsa ta cikin bidiyon da take ɗauka a wani lungu da ke harabar jami’ar.

Cikin takardar korar da jami’ar ta fitar mai ɗauke da kwanan watan 13 ga watan Fabrairu, wadda magatakardar jami’ar, Victor I. Modebelu ya sanya wa hannu, ta ce an ɗauki matakin ne bayan shawarar kwamitin bincike da jami’ar ta kafa.

Karanta Wannan  Yadda 'yan tà'àddà suka kàshè sojoji suka kwashe màkàmài a sansanin soji a Borno, Sojojin dai sun tsere yayin da màhàràn suka afkawa sansanin nasu, saidai da gari ya waye sun koma, Kalli bidiyon Yanda sojojij ke kuka, da hotunan gawarwakin wadanda aka kashe birjik a kasa

”Kwamitin ya samu ɗalibar da laifin saɓa wa dokokin ladabtarwa na jami’ar, musamman sashe na 4 na dokar ladabtarwa ta (SDR)”, in ji takardar korar, kamar yadda Jaridar Punch ta ruwaito.

Bidiyon cakumar malamin ya ja hankalin mutane da dama a shafukan sada zumunta, inda aka yi ta kiraye-kirayen ɗaukar mataki.

Jami’ar ta buƙaci ɗalibar ta gaggauta ficewa daga harabar makarantar tare da mayar wa jami’ar duk wasu abubuwan da ke hannun ɗalibar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *