Monday, March 24
Shadow

Makiyanane ke wannan karyar: Sanata Akpabio yace bai rabawa sanatoci dala Dubu 5 ba dan su goyi bayan dakatar da gwamnan Rivers ba

created by photogrid

Sanata Godswill Akpabio a kokarin kare kansa daga zargin da ake masa na raba dala dubu 5 da dubu 10 ga wasu sanatoci dan su goyi bayan dakatar da gwamnan jihar Rivers yace makiyansa ne ke yada wannan maganar.

An dai yi zargin cewa, Sanata Godswill Akpabio ya kira sanatocin zuwa shan ruwa a gidansa inda a canne ake zargin ya raba musu kudaden.

Saidai a martani ta bakin kakakinsa, Hon. Eseme Eyiboh yace makiya ne ke yada wannan jita-jitar.

Yace dama can al’adace ta Sanata Godswill Akpabio ya shiryawa sanatoci shan ruwa duk shekara, shekarar data gabata yayi a wannan shekarar ma yayi.

Amma maganar raba daloli babu ta.

Karanta Wannan  'Yan Bindiga sun budewa motar matafiya wuta a hanyar Sokoto zuwa Minna, 2 sun Mùtù wasu sun jikkata

An dai zargi cewa ministan Abuja, Nyesome Wike ne ya kaiwa Sanata Godswill Akpabio Dala Miliyan $3 dan ya rabawa sanatocin.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *