Friday, December 5
Shadow

Malamai sun sauke Qur’ani a Kano dan nasarar Shugaba Tinubu a 2027 da kuma takarar Gwamna ta Sanata Barau Jibrin

Rahotanni daga jihar Kano na cewa an gudanar da addu’ da yankan Dabbobi sannan an sauke Qur’ani saboda neman Allah ya baiwa shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu da Sanata Barau Jibrin Maliya nasara a 2027.

Rahoton yace an yi wanan taronne a gidan Baballiya dake Kurna karamar hukumar Fagge dake Kano.

Kuma mutane daga kowacce karamar hukumar a jihar sun samu halarta.

Bayan kammala saukar Qur’anin, an gabatar da addu’a ga Shugaba kasa, Bola Ahmad Tinubu da Sanata Barau Maliya kan Allah ya basu nasara.

Sannan kuma malaman sun yi Addu’ar Allah ya bada zaman lafiya, ci gaban tattalin arziki a Najeriya baki daya.

Karanta Wannan  Atiku ya caccaki manufofin Tinubu kan ƙayyade shekarun shiga jami’a

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *