
Rahotanni sun ce malaman jinya 16,000 ne wanda suka yi karatu a Najeriya suka tsere zuwa kasar Ingila suke aiki a can.
Hakan ya farune a tsakanin shekarun 2017 zuwa 2025.
Kuma Rahoton yace hadda Ungozoma ne ke tserewa daga Najeriyar zuwa kasar Ingila.
An samu wannan bayanai ne daga rijistar da kasar Ingilar ta fitar.
Wannan na nuni da cewa, Najeriya na fuskantar karancin malaman jinya yayin da ‘yan kasar ke tserewa zuwa kasashen Turai dan aiki a can saboda albashi me kyau da ake biya acan din.