
Manyan Malaman cocin Katolika 2 da ake tsammanin na daga cikin wanda zasu gaji Fafaroma Francis ana zarginsu da yin rufa-rufa game da binciken cin zarafin kananan yara.
Malam sune Cardinal Pietro Parolin dan kasar Italiya, sai Cardinal Luis Antonio dan kasar Philippines.
Wata kungiya dake saka ido kan irin wannan lamari ta kasar Amurka, The American watchdog Bishop Accountability ce ta bayyana hakan inda tace duka malaman biyu ana zarginsu da yin rufa-rufa wajan binciken malaman cocin da aka kama da lalata da kananan yara.
Daya daga cikin shuwagabannin wannan kungiya me suna Anne Barrett Doyle ta bayyana cewa, an kaiwa Cardinal Pietro Parolin korafe-korafen cin zarafin yara ta hanyar lalata dasu da suka faru a kasashen Duniya daban-daban amma sai yayi rufa-rufa yaki bin diddigin lamarin ko kuma ya kawo tarnaki a binciken, dan haka tace ba za’a amince dashi a matsayin fafaroma ba.
Hakanan ta kuma zargi Cardinal Luis Antonio Tagle da cewa shima bai yi abinda ya kamata ba wajan binciken cin zarafin yara ba a kasarsa ta Philippines.
Saidai tuni kasar Philippines ta fito ta wanke Cardinal Luis Antonio Tagle inda tace bashi da hurumin daukar wani mataki game da matsalar cin zarafin yara a tsakanin malaman cocin.