Friday, December 5
Shadow

Manyan Sojoji sama da 500 ne aka tursasawa yin ritaya a tsakanin Gwamnatocin Buhari dana Tinubu

Rahotanni sun bayyana cewa, Manyan Sojoji sama da 500 ne aka yiwa ritaya a tsakanin gwamnatocin Tsohon Shugaban kasa, Muhammadu Buhari da Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu.

Rahoton yace Sojojin sun Hada da janarori manya da kanana.

Wata majiya daga gidan soji ta shaidawa jaridar Punchng cewa, yawan manyan sojojin da akawa ritayar dole sun kai 900.

Lamarin ritayar dole na faruwane idan aka nada sabbin shuwagabannin sojoji, dan haka wadanda ke gaba da sabbin shuwagabannin sojojin dole su yi ritaya dan a samu aiki ya daidaita.

Karanta Wannan  Daga almajiranci na zama shugaban NNPC - Kyari

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *