Friday, December 5
Shadow

Masu zanga-zanga sun shirya tsaf dan nunawa shugban kasa, Bola Ahmad Tinubu fushinsu a yau ranar Dimokradiyya

Rahotanni sunce akwai artabu da dauki ba dadi da akw tsammanin zau faru a yau tsaanin masu zanga-zanga da jami’an tsaro a majalisar tarayya dake Abuja.

Masu zanga-zangar ta ranar ‘yanci shin shirya zanga-zangar a Abuja dama gurare 19 a fadin kasarnan.

A yau ne ake sa ran shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu zai halarci majalisar tarayya dan karrama wasu ‘yan majalisar sannan a canne zai gabatarwa da ‘yan kasa jawabi.

A baya dai, shugaban kasar ya so ya gabatar da jawabin ga ‘yan kasa da safiyar Ranar Alhamis amma daga baya aka canja tsari aka ce sai ya je majalisar tarayya.

Maau zanga-zangar sun ce zasu gabatar da kokensu ne game da matsalar matsim tattalin arzikin da talakawa ke ciki.

Karanta Wannan  Da Duminsa: Ji yanda Jirage 15 sun makale a sararin samaniyar jihar Katsina suna shirin sauka dan halartar jana'izar Buhari amma ba wuri

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *