Wata matar aure me suna Iyanu Adedeji ‘yar kimanin shekaru 22 ta kashe mijinta me suna Funsho Jimoh dan kimanin shekarun 28.
Lamarin ya farune a yankin Gbonogun dake Abeokuta jihar Ogun.
Ma’auratan dai na da yara 2.
Rashin jituwar ta farane bayan da mijin ya zargi matar tasa da vin amanarsa inda ta karyata, rikici ya kaure inda ta dakko wuka ta daba masa.
Daga nan ne ta daukeshi zuwa asibitu inda likita ya tabbatar da ya mutu.
Kakakin ‘yansandan jihar, Omolola Odutola ta tabbatar da faruwar lamarin inda tace wadda ake zargin tana hannu ana kuma ci gaba da abincike.