
Tauraruwar fina-finan Hausa, matar Rarara, Aishatulhumaira ta aikewa da abokin aikinta kuma dan Tiktok, Baana sammace daga ofishin DSS.
Aisha ta kai korafin cewa, Baana ya wallafa Bidiyon inda ya mata Qazabin yin ma’amalar da bata dace ba da maza ciki hadda shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu.
Sannan tace a cikin Bidiyon ya zargi mijinta da aikata Alfasha da matan mutane.
Tace wannan ba karamin abu bane musamman ma saka sunan shugaban kasa a ciki wanda tace zai iya haifar da matsalar tsaro.