
Wannan mutumin me suna Adamu Yusuf ya rasa iyalansa guda 9, matarsa daya da jaririn dansa da ‘yan uwansa 6 a ambaliyar ruwan da ta faru a Mokwa dake jihar Naija.
Shi ya fitone daga Tiffin Maza daya daga cikin kauyukan da lamarin ya fi shafa.
Yace da suka ji ruwan, sun fito waje inda yake kowa ya rike hannun kowa yace amma da ruwan yayi karfi sai ya tarwatsasu, yace yana ji yana gani haka ruwan ya tafi da iyalinsa.
Yace shima Allah ne ya tseratar dashi saboda ya iya ruwa.
Yace kayan dake jikinsa ma taimako aka bashi.