Bincike ya nuna cewa, matasa dake tsakanin shekaru 21 zuwa 30 ne a Najeriya suka fi amfani da maganin karfin maza .
Yawanci ana sayen magungunan kara karfin maza ne dan samun kuzari da jin dadin jima’i.
Saidai da yawa daga cikin magungunan da ake sayarwa din basu da rijista hukukomin lafiya na kasa basu tantance su ba, hakanan kuma mafi yawan masu sayar da magungunan ma basu da ilimi akan harkar maganin.
Hakan yasa ake samun matsalar magungunan su rika bayar da illa ga lafiyar dan adam inda akan samu matsalar mazaje na mutuwa yayin jima’i.