
Rahotanni daga jihar Legas sun bayyana cewa, matasa a jihar Legas din sun fito zanga-zangar adawa da wasu tsare-tsaren gwamnatin shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu.
Haka lamarin yake ma a jihar Rivers, matasa sun fito inda suka hau kan tituna suna nuna rashin amincewarsu da tsare-tsaren gwamnatin musamman dakatar da gwamnan jihar Rivers da kuma dokar sanya ido akan kafafen sada zumunta.
‘Yansandan dai sun yiwa matasan rakiya tare da basu Kariya musamman a Legas, a baya dai hukumar ta ‘yansanda ta hana matasan fitowa zanga-zangar inda suka ce ba’a sakawa zanga-zangar lokacin da ya dace ba.
Hakanan a jihar Oyo, da babban birnin tarayya, Abuja ma, masu zanga-zangar sun fito sun nuna damuwarsu.