Wednesday, January 15
Shadow

Matata na lakada min dukan tsiya, Magidanci ya kai kara kotu a raba aurenshi da matarsa

Wani magidanci me suna Saka ya kai matarsa me suna Sadia kara kotu inda yake neman a raba aurensu saboda tana shan giya da dukansa da fitsarin kwance.

Saka yace auren Sadia yasa ya rasa farin ciki inda yake zaune cikin kuncin rayuwa.

Yace har Naira 50,000 ya bata dan ta fara kasuwanci amma ta kashe kudin wajan shan giya.

Yace a kowane lokaci bayan ta sha giya, haka take zuwa ta kwanta ta rika fitsari akan gadonsu.

Yace a duk lokacin da yayi korafi akan abinda take aikatawa takan kulleshi a daki ta rika lakada masa duka.

Yace ya kaita wajan ‘yansanda sau da yawa amma taki dainawa shine yace bari ya kai karanta kotu.

Karanta Wannan  Abincin dake gina jiki

Saidai matar itama tace ta gaji da auren a rabasu kawai, tace mijin nata bai cika hakkinsa na daukar nauyinta, Naira Dari 2 kawai yake bata.

Saidai tace kotu ta ce ya sama mata gurin zama dan bata da inda zaka kai kayanta.

Saidai mai shari’a na kotun Customary dake Mapo a Ibadan jihar Oyo, Mrs S.M Akintayo ya bayyana cewa, ya daga sauraren shari’ar sai nan gaba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *