
Wani mutum me suna Alhaji Yikangi daga kauyen Chikan na karamar hukumar Gbako jihar Naija ya kashe bazawarin tsohuwar matarsa me suna Muhammad Ma’aba.
Alhaji Yinka yawa matarsa me suna Fatima Suleiman saki 3 wanda bisa tsarin addinin Musulunci ba zai iya sake aurenta ba sai bayan ta sake yin wani auren ta fito.
Saidai Alhaji Yinka ya sha Alwashin matar tasa saidai ta dawwama ba aure dan kuwa ba zai barta ta yi auren ba.
Rahoton yace ya jagoranci mutane inda sukawa Muhammad Ma’aba Kwantan Bauna suka ta dukansa har sai da ya mutu.
Kakakin ‘yansandan jihar, SP Wasiu Abiodun ya tabbatar da faruwar lamarin inda yace suna bincike dan kama duka masu hannu a lamarin.