
Matar kakakin majalisar Dattijai, Unoma Akpabio ta maka Sanata Natasha Akpoti a kotu bisa zargin bata suna da take hakkin bil’adama.
Ta kai Sanata Natasha Akpoti babbar kotun tarayyane dake Abuja.
Hakan ya biyo bayan zargin da sanata Natasha Akpoti tawa Akpabio na cewa ta fara samun matsala a majalisar ne tun bayan da ta ki yadda ta yi lalata da da sanata Akpabio.
Matar sanata Akpabio ta bayyana cewa, zargin da Sanata Natasha Akpoti tawa mijinta yasa ita da ‘ya’yanta sun shiga firgici da kuma tsoron za’a iya kai musu harin da zai iya sawa su rasa rayuwarsu.
Dan haka matar Akpabio ta nemi kotun da ta ayyana maganar da Sanata Natasha Akpoti ta yi a matsayin take hakkin mutuncin mijinta.
Sannan ta nemi kotun data tursasa Sanata Natasha Akpoti ta biya diyyar Naira Biliyan 250 akan zargin karyar da ta yi sannan kotun ta hana Sanata Natasha Akpotin ci gaba da magana akan lamarin.
Sannan tace kotun ta tursasa Sanata Natasha Akpoti ta fito Duniya ta bayar da hakuri.