Friday, March 14
Shadow

Minista ya yi barazanar barin APC idan ba a sauya shugabancinta na Kano ba

Minista a ma’aikatar gidaje, Yusuf Abdullahi Ata ya yi barazanar cewa shi da magoyansa za su iya ficewa daga jam’iyyar APC a Kano, matuƙar ba a canja shugabancin jam’iyyar a jihar ba.

Ministan ya ce furucin jagoran jam’iyyar ne ya jawo faɗuwar jam’iyyar a zaɓen da ya gabata na 2023, kamar yadda ya bayyana a wani faifan bidiyo da ya karaɗe kafofin sadarwa, wanda aka ce ya yi a taron masu ruwa da tsaki na ƙaramar hukumarsa ta Fage a jihar Kano.

Ata ya ce, “muna faɗa wa kowa, idan aka mayar da irinsu, duk irinmu fita za mu yi.”

Ya ƙara da cewa, “mu an mana tarbiya, mun san waye malami, mun san waye babba. Saboda haka ba za mu sauka daga turbarmu ba. Idan suka dawo da shi, mu za mu fita, kuma na rantse da Allah sai jam’iyyar ta sake faɗi zaɓe,” in ji shi.

Karanta Wannan  A karshe dai bayan shan ruwan Allah wadai, Gwamnatin tarayya na shirin yafewa kananan yaran data kai kotu bosa zargin cin amanar kasa

“Dole a canja, dole a nemo mutanen kirki masu mutunci a ba su saboda ya zama tare da mu, ya yi sha’awar ya sake ba mu.”

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *