Mu a Akwa Ibom Tinubu za mu yi a 2027 – Akpabio

Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio, ya ce dukkan jam’iyyun siyasa a jihar Akwa Ibom sun hade wuri guda.
Ya kara da cewa wannan hadin gwiwa zai mara wa Shugaba Bola Tinubu baya domin sake tsayawa takara, da Gwamna Umo Eno na jihar, da kuma shi kansa Akpabio.
Akpabio ya bayyana hakan ne a ranar Juma’a yayin taron rabon tallafi ga al’ummar mazabarsa da kuma kaddamar da ayyuka a Ikot Ekpene, yankin Akwa Ibom na arewa maso yamma.
“Yayin da nake magana da ku yanzu, babu wani abin da ake kira jam’iyya a jihar Akwa Ibom a shekarar 2027,” in ji shi.
“Don kujerar majalisar dattawa ta yankin Ikot Ekpene, dukkan jam’iyyun siyasa sun hade don kada kuri’unsu ga Sanata Godswill Akpabio.
“Kujerar gwamna a shekarar 2027, dukkan jam’iyyun siyasa sun yarda da kada kuri’a ga Gwamna Umo Eno.
“Jihar Akwa Ibom ta kuduri aniyar kada kuri’a ga Shugaba Bola Tinubu, Eno a matsayin gwamna na jihar, da kuma Sanata Akpabio a majalisar dattawa.
“Jam’iyyar PDP ta tarwatse, kuma laimar ba za ta iya kare kowa ba.”