
Wani Jigo a jam’iyyar APC ya bayyana cewa, jam’iyyarsu ce ke da alhakin rikicin dake faruwa a jam’iyyun Adawa.
Hon. Farouk Adamu Aliyu ne yayi wannan magana inda yace sun yi hakanne kamin zuwa zaben shekarar 2027.
Wannan magana tasa dai ta zo daidai da Hasashen da mutane ke yi na cewa dama APC ce ke hana jam’iyyun Adawar zaman lafiya dan kada su bata kalubale.
Ya bayyana hakanne hirar da aka yi dashi a gidan Talabijin na AIT.
Yace tabbas sune ke hana jam’iyyun na adawa zaman lafiya dan ba zasu bari su kwace mulki a hannunsu ba, yace a yanzu ma babu wata jam’iyyar Adawa ta gaskiya duk suna hauragiya ne amma babu wata jam’iyyar adawa da zata iya kwace mulki a hannun APC, saidai watakila nan gaba.