Saturday, March 15
Shadow

Mummunan hadari yayi sanadiyyar mùtùwàr Mutane 12, wasu sun jikka a jihar Naija

Wani mummunan Hadarin da ya faru a jihar Naija yayi sanadiyyar mutuwar mutane 12 inda wasu kuma suka jikkata.

Lamarin ya farune akan titin Agaie zuwa Lapai.

Kwamandan hukumar kiyaye hadura ta jihar, FRSC, Kumar Tsukwam ya tabbatarw da manema labarai hakan a sanarwar da ya fitar ranar Asabar a Minna.

Yace har yanzu ma’aikatansa na wajan da hadarin ya faru inda yace zasu tattaro bayanai su bayar game da hadarin.

Wani da ha shaida yanda abin ya faru, ya gayawa majiyarmu cewa, 3 daga cikin wadanda suka mutu ‘yan gida dayane.

Sannan sun ce hadarin ya farune a yayin da wata motar Bas ke tafiya daga Minna zuwa Katcha ta yi taho mu gama da wata trela a daidai kauyen Jippo dake kusa da Mashina.

Karanta Wannan  Bidiyon yanda aka kunyata wasu da aka kama suna lalata

Wanda suka jikkata ciki hadda direban suna karbar kulawa a asibitin Lapai General Hospital. Direban motar,Mohammed Baba yace hadarin ya farune a yayin da Tirelar ke kokarin wuce wata mota.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *