
Shugaban sojojin Najeriya, Christopher Musa ya baiwa sojojin Umarnin cewa duk inda aka kaisu aiki kada su sake jiran wai sai an basu umarnin yin harbi.
Yace idan suka ga yankin da aka kaisu aiki na cikin barazana, su dauki mataki, idan suka ga gini ko ma’aikatar da aka kaisu aiki na cikin barazana su dauki mataki, idan suka ga abokin aikinsu na cikin barazana su dauki mataki hakanan idan suka samu kansu a cikin barazana su dauki mataki.
Shugaban sojojin yace bai son wani soja ya kara bashi uzurin cewa wai an yi abinda bai dace ba a kusa dashi ko kuma an kai Hhàriy a kusa dashi bai dauki mataki ba yace masa wai saboda ba’a bashi umarni bane, yace kada sojojin su sake jiran umarni.
Sannan ya gargadi kwamandojin sojojin da cewa duk wanda aka samu barakar aikata ba daidai ba a rundunarsa zai dandana kudarsa.
Saidai kuma yace wanda ya nuna bajinta zai samu karin girma.
Me zaku ce game da hakan?