
Sojojin kasar Israyla sun bayyana cewa, sun ci gaba da kaiwa kasar Iran hari.
Hakan na zuwane bayan da a baya muka kawo muku rahoton cewa, an ga jiragen yakin kasar Israyla na ci gaba da shawagi a sararin samaniyar kasar Iran.
Sun samu wannan nasarar ne bayan lalata makaman dake kakkabo jiragen sama na kasar ta Iran.
Kasar ta Israela tace kamata yayi ta kammala kaiwa Iran hari a cikin kwanaki 2 amma sun ga alamu na nuni da cewa harin zai iya kai akalla sati biyu suna kaiwa.