
Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya bayyana cewa, sun cimma yawan kudin shigar gaba dayan shekarar 2025 da ake bukata.
Shugaban ya bayyana hakane a wajan wani taro inda yace kuma kudin ba ta bangaren man fetur suka zo ba.
Yace kuma a yanzu Najeriya babu wani bankin cikin gida da yake binta bashi.