
Hukumar ‘yansandan jihar Bauchi ta sanar da dakile yunkurin barkewar rikicin addini tsakanin mabiyan wasu kungiyoyin addinin Musulunci 2.
Hukumar tace hakan ya farune awanni kadan bayan rasuwar babban malamin addinin Islama a garin Dutsen Tanshi watau Dr. Abdulaziz Idris.
Kwamishinan ‘yansandan jihar, Mr Sani-Omolori Aliyu ya yi kiran a kwantar da hankula sannan a gudanar da bincike kan faruwar lamarin.
A sanarwar da kakakin ‘yansandan jihar, CSP Ahmed Wakili, ya fitar yace rikicin ya barkene bayan kalaman limamin masallacin Galli yayi kalamai da ake zargin na tayar da fitinane akan marigayi Dr. Abdulaziz Idris Dutsen Tanshi.
Yace mabiyan marigayin sun je masallacin inda suka yi yunkurin gudanar da zanga-zanga, saidai tuni ‘yansanda suka kai dauki suka watsa masu zanga-zangar cikin lumana suka baiwa limamin masallacin da mabiyansa kariya.
Daga baya an baiwa limamin kariya.
Kwamishinan ‘yansandan jihar, Aliyu yayi kira ga shuwagabannin addini da su rika kiyaye abinda zasu rika fadawa mabiyansu.