Friday, December 5
Shadow

Mun Gama Ýanke Shawarar Mayar Da Tinubu Jihar Legas A Zaben 2027, Domin Za Mu Dakatar Da Shi Daga Zarcewa A Mulki Karo Na Biyu, Inji El-Rufai

Mun Gama Ýanke Shawarar Mayar Da Tinubu Jihar Legas A Zaben 2027, Domin Za Mu Dakatar Da Shi Daga Zarcewa A Mulki Karo Na Biyu, Inji El-Rufai.

Daga Comr Nura Siniya

Tsohon Gwamnan Jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufai, ya bayyana cewa akwai wani muhimmin yunkuri na kafa hadaka da nufin ganin an dakatar da Shugaba Bola Ahmed Tinubu daga sake samun mulki a karo na biyu.

Malam Nasiru El-Rufai ya bayyana hakan ne a yayin taron baje kolin fasaha da ƙirƙira na “Arewa TechFest da aka gudanar a jihar Katsina ranar Laraba 21 ga watan Mayu 2025.

A cewarsa, “Jiya da karfe 8 na dare, mun gudanar da wani muhimmin taro na hadakar da muke kokarin kafa wa domin tabbatar da cewa Shugaba Tinubu ya koma Legas.”

Karanta Wannan  Likitoci sun mana kadan matuka duk sun tsere kasashen waje>>Jihar Kwara ta koka

Duk da wannan yunkuri, El-Rufai ya jaddada cewa akwai ministocin da suke ganin sun cancanci ci gaba da aiki, inda ya ambaci Ministan Sadarwa da Fasahar Zamani, Bosun Tijani, a matsayin daya daga cikinsu. “Mun yanke shawarar cewa za mu ci gaba da rike Bosun Tijani, za mu barshi a matsayin minista domin yana yin aiki mai kyau,” in ji shi.

Wannan jawabi ya jawo ce-ce-ku-ce a kafafen sada zumunta, musamman duba da irin rawar da El-Rufai ke takawa a harkokin siyasar Najeriya da kuma yadda yake tasiri a shiyyar Arewa.

Taron Arewa TechFest dai wani babban taro ne da ke hada matasa, masana kimiyya, da ‘yan kasuwa domin karfafa bangaren fasahar zamani a Arewacin Najeriya.

Karanta Wannan  Sanata Kabiru Marafa ya fice daga jam'iyyar APC, kalli Bidiyon jawabinsa

Sai dai El-Rufai ya yabi ministan matasa na Tinubu Basoum Tijjani inda yace yana ƙoƙari za su bar shi kan mukaminsa idan har suka maida Tinubu Lagos.

Ya kuke kallon wannan batu?

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *