
Jam’iyyar APC ta mayar da martani akan maganganu da avubuwan da tsohon gwamnan jihar Kaduna Malam Nasiru Ahmad El-Rufai ke yi.
Kakakin APC, Ajibola Basiru ne ya bayyana hakan a wata ganawa da yayi da manema labarai inda yace abinda ke damun El-Rufai shine da bai samu ya zama minista a Gwamnatin Tinubu ba.
Yace daga nan ne sai El-Rufai ya koma sukar Gwamnatin Tinubun, yace amma abinda ke musu dadi shine a Arewar ma shi ba wani me fada aji bane.
Ya kara da cewa, El-Rufai na ta kokari ne kawai yaga ya kawo tarzoma da raba kai tsakanin Arewa da kudu, ta wannan hanyar ne yake son yin suna.
Tsohon Gwamnan na Kaduna dai sunansa ya fito a cikin mutanen da Tinubu yaso ya nada a matsayin ministoci amma da yaje majalisa sai ya kasa tsallake tantancewar da aka yi kokarin yi masa.
bayan nan an ga El-Rufai ya je yana ta bibiyar tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar wanda a baya ana ganin dangantaka tsakaninsu ta yi tsami. Ko da gaisuwar mutuwar Edwin Clark, El-Rufai tare suka je da Atiku inda kuma suka je suka yi sallar Juma’a tare.
Hakanan a Kaduna ma an ga yanda El-Rufai ya gana da wakilan Jam’iyyar PDP wanda ake tsammanin ko zai koma Jam’iyyar ne.