
Ministan Sufurin jiragen sama, Festus Keyamo ya yi martani ga komawar hadakar ‘yan jam’iyyar Adawa musamman daga APC zuwa ADC.
Keyamo yace ‘yan APC din da suka koma ADC a jiya sune munafukan cikin APC da suka munafurci shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu a zaben 2023 basu so ya ci zabe ba.
Manya-manyan wadanda suka koma ADC wadanda ‘yan APC ne sun hada da Rotimi Amaechi da Abubakar Malami da kuma Malam Nasiru Ahmad El-Rufai wanda shi dama ya dade da ficewa daga jam’iyyar ta APC zuwa SDP
Keyamo yace komawarsu ADC bai ragi APC da komai ba sai ma kara karfi da jam’iyyar ta yi.
Festus Keyamo ya kara da cewa sauran wadanda suka koma ADC wadanda suka nemi takarkaru ne amma basu samu nasarar ci ba.