Sunday, March 16
Shadow

Mun kusa fara biyan alawus ɗin naira 77,000 – NYSC

Hukumar NYSC ta ce ta kusa fara biyan masu yi wa ƙasa hidima alawus ɗin naira 77,000.

Hukumar ta bayyana haka ne a matsayin martani kan rashin fara biyan sabon alawus ɗin bayan an sanar da ƙari daga naira 33,000 da ake biya biyo bayan ƙara mafi ƙanƙantar albashi.

A watan Yulin shekarar da ta gabata ne gwamnatin tarayya ta yi alƙawarin fara biyan sabon alawus ɗin, amma har yanzu ba a fara biya ba, kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito daga masu bautar ƙasar.

A watan Janairu, darakta-janar na NYSC, Birgediya-janar Yushau Ahmed ya sanar da cewa daga watan Fabrairu za a fara biyan sabon alawus ɗin, amma kuma ba a biya ba a watan na Fabrairu da ya gabata.

Karanta Wannan  Sai da Buhari ya amince sannan na bar APC zuwa SD, Saboda babu wani abun da nake yi ba tare da na sanar da shi ba>>El-Rufai

Daraktan riƙo na hulɗa da jama’a na hukumar, Caroline Embu, ta ce suna jiran kuɗi ne da umarni kafin fara biyan sabon alawus ɗin, duk da cewa ba ta bayyana zuwa yaushe ba.

Sai dai ta ce duk shirye-shiryen da suka kamata a yi, duk an yi, “jiran lokaci kawai ake yi.”

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *