Friday, December 26
Shadow

Mun raba kudin Talli Naira Biliyan 330 ga gidaje Miliyan 8.5 a Najeriya>>Inji Ministan kudi

Gwamnatin tarayya tace ta rabawa gidaje Miliyan 8.5 Tallafin kudi Naira Biliyan 330 a fadin Najeriya.

Ministan kudi, Wale Edun ne ya bayyana hakan.

Ya bayyana hakane ranar Laraba a Abuja inda yace gwamnati ta dawo da raba tallafin bayan Gyare-Gyaren da aka wa tsarin.

Yace suna raba kudadenne saboda ragewa mutane radadin tsadar rayuwa inda yace mutane Miliyan 15 suke son rabawa.

Yace zuwa yanzu sun raba kudin a gide Miliyan 8.5 inda suke biyan Naira dubu shirin da biyar duk wata.

Ministan yace sauran ma zuwa karshen shekarar nan za’abasu.

Karanta Wannan  In kunga dama ku ce Maula nakewa Ahmed Musa dan nace ya bani kyautar Naira Miliyan 10, ina sake nanatawa ina rokon ya bani Naira Miliyan 10>>Inji Mansurah Isah

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *