
Rundunar sojin Najeriya ta ce sojojinta na Operation HADIN KAI (OPHK) sun kashe mayaƙan Boko Haram da dama a wani samame da suka ƙaddamar a dajin Sambisa da ke jihar Borno.
Wannan aikin, a cewar sanarwar da shalkwatar sojojin ta fitar ta ce ya gudana ne a ranar 11 ga watan Mayu, 2025, a yankin Ladin Buttu, “wurin da aka san shi da zama mafakar ’yan ta’adda” kuma rundunar sojin ta bayyana nasarar a matsayin muhimmin ci gaba a yaƙin da ake yi da ƙungiyar Boko Haram a Arewa maso gabashin ƙasar.
Hakan na zuwa ne bayan sabbin hare-haren da mayaƙan Boko Haram suka ƙaddamar kan wurare daban-daban a jihar Borno, inda matsalar rikicin Boko Haram ta fi ƙamari.
A sanarwa da rundunar ta wallafa a shafinta na X, mataimakin daraktan hulda da jama’a na Sojojin, Kyaftin Reuben Kovangiya, ya tabbatar da cewa sojojin sun yi arangama da ’yan ta’addan cikin kazamin fada.
“Sojojin sun yi amfani da ingantattun makamai da dabaru, lamarin da ya ba su nasara wajen kashe da dama daga cikin ’yan ta’addan, yayin da wasu suka tsere da raunukan harbin bindiga.” in ji sanarwar.
An kuma ƙwato makamai da kayan yaki masu tarin yawa, kamar yadda sanarwar ta bayyana.
Ladin Buttu na daya daga cikin muhimman sansanonin mayaƙan Boko Haram a yankin, “inda su ke amfani da shi wajen tsara dabaru da adana kayayyaki, da ƙaddamnar da hare-hare.”
Kyaftin Kovangiya ya bayyana cewa wannan aiki ya yi daidai da umarnin sabon shugaban Hafsan Sojin Kasa na ƙara kaimi wajen kai hare-hare da rushe cibiyoyin Boko Haram a yankin.