Friday, December 5
Shadow

Mutane 2 sun nutse a ruwa suka ràsù a Kano yayin da suke bin sahun wani da suke bi bashi

Wasu mutane 2 a Kano sun rasu bayan da suka nutse a ruwa yayin da suke bin sahun wani da suke bi bashi.

Lamarin ya farune a titin Ring Road dake Dorayi Babba.

Kakakin hukumar kwanakwana ta jihar, ACFO Saminu Yusif Abdullahi ya tabbatar da faruwar lamarin.

Yace wani me suna Garba Sani ne ya kirasu ya sanar dasu lamarin da misalij karfe 9:36 a.m.

Yace sun dakko mutanen 2 masu suna Saifullahi Muhammad, 27, da Halifa Abdullahi, 29 daga ruwan da suka fada.

Yace suna bin wani mutum ne da suke bi bashi daga Kofar ruwa yayin da ibtila’in ya afka musu.

Yace an kaisu asibitin Murtala Inda likita ya tabbatar da sun rasu, yace sun mika gawarwakin zuwa ga Inspector Halifa Muhammad.

Karanta Wannan  Rikicin Jam'iyyar NNPP: Gwamna Abba Gida-Gida yaki daga waya bayan sa Kwankwaso ya kirashi

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *