Mazauna Karamar Hùkumar Talata Mafara Šùn Yabawa ShugabaTinubu Da Matawalle Kán Hallaka Ŕìķakkun ‘Ýan Bìñdiga Jijji Da Kachallah Sagili.

Mazauna karamar hukumar Talata Mafara da ke jihar Zamfara sun bayyana godiya mai yawa ga shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu, Ministan kasa a ma’aikatar tsaron Nijeriya Dr Bello Matawalle, Mai ba shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro Malam Nuhu Ribadu, da Babban hafsan hafsoshin Nijeriya Janar Christopher Musa, bisa irin gudummawar da suka ba da wajen kawar da wasu manyan shugabannin ‘yan bindiga a Arewa maso Yammacin Nijeriya da ma sauran sassan kasar.
Aikin da aka kaddamar domin fatattakar Jajji Dan Auta da Kachallah Sagili ya samu yabo daga al’umma a matsayin wata babbar nasara da ke nuni da dawowar zaman lafiya a yankin da ake fama da rikici.
Yakubu Ibrahim Mafara, wanda ya yi jawabi a madadin al’ummar Talata Mafara, ya fitar da wata sanarwa a ranar Juma’a yana yaba wa kokarin hadin guiwa da gwamnatin tarayya da jami’an tsaro suka yi.
“Muna matukar godiya ga Matawalle, ShugabaTinubu, NSA da sauran jami’an tsaro,” in ji shi, yana bayyana farin cikin da jama’a ke ciki bayan kammala aikin.
Sanarwar ta bayyana tasirin wannan aiki a kan al’ummar yankin, wadda tsawon shekaru tana cikin fargaba da wahalhalu, sakamakon hare-haren da ‘yan bindiga ke kai wa a jihar Zamfara.
Aikin ya gudana ne a ranar Alhamis a Unguwar Maikwanugga da ke cikin karamar hukumar Talata Mafara, inda dakarun tsaro tare da hadin guiwar kungiyoyin sa-kai suka gudanar da sintiri na musamman a yankin Mafara.
A cewar sanarwar, rahotanni sun tabbatar da cewa an kashe Jijji Dan Auta da Kachallah Sagili — shugabannin ‘yan bindiga da ake zargi da kai hare-hare, sace mutane da karbar kudin fansa a yankin.
“Mutuwarsu na da matukar tasiri ga al’umma da suka dade suna fama da tashin hankali da rashin tsaro,” in ji Yakubu.
“Kisan Jijji Dan Auta ya sauya yanayi a cikin garinmu; ya kawo nutauwa,” in ji shi, yana wakiltar muryar mutanen da suka shafe shekaru a karkashin barazanar ‘yan bindiga.
Ana kallon aikin a matsayin martanin kai tsaye ga yawaitar hare-haren da ke faruwa a jihar Zamfara, inda kungiyoyin masu dauke da makamai ke addabar kauyuka, suna lalata rayuwar jama’a da raba su da muhallansu.
Godiya daga jama’ar yankin na nuna yadda ake samun karuwar amincewa da jajircewar gwamnatin tarayya wajen yaki da rashin tsaro a yankin Arewa maso Yammacin Nijeriya.
A halin yanzu, aikin ya kasance hadin guiwa tsakanin dakarun sojin Nijeriya da kungiyoyin sa-kai, wadanda ke a wajen tattara bayanan sirri da kare al’umma.
Sintirin da aka yi a yankin Talata Mafara ya kasance wani bangare na shirin kawar da sansanonin ‘yan bindiga da dawo da zaman lafiya a jihar Zamfara — wadda ta kasance cibiyar ayyukan ta’addanci da satar mutane cikin ‘yan shekarun nan.
“Kashe Jijji Dan Auta da Kachallah Sagili ana sa ran zai raunana damar da ‘yan bindiga ke da ita wajen ci gaba da kai hare-hare a yankin.”