
Kauyuka da yawa ne suke biyan ‘yan Bindiga kudaden Haraji a jihar Zamfara dan kada su kai musu hari ko su yi garkuwa dasu.
A shekarar 2025 dinnan da muke ciki kawai, watau daga watan Janairu zuwa yanzu Mutanen jiha Zamfarar sun biya ‘yan Bindiga jimullar Harajin Naira Miliyan 500, kamar yanda jaridar Daily Trust ta bayyana.
A watan Janairu kawai, marigayi dan Bindiga Isuhu Yellow, ya kakabawa mutanen kauyuka 25 harajin Naira Miliyan 172.7.
Hakanan shima Dogo Gide ya kakabawa kauyuka 23 Harajin Naira Miliyan 100.
Lamarin ‘yan Bindiga dai na ci gaba da ta’azzara duk da ikirarin kokarin da gwamnati ke cewa tana yi.