
Tsohon shugaban kasa, Olusegun Obasanjo ya bayyana damuwa kan yanda Darajar Najeriya ta zube a Idon Duniya inda yace a lokacin mulkin sa da Marigayi Janar Murtala, Kasar Amurka basa daukar wani mataki a Afrika ba tare da Sanar da Najeriya ba.
Ya bayyana hakane a Abeokuta ranar Litinin yayin ganawa da wasu matasa.
Obasanjo yace shi da Murtala sun dawo da Martabar Najeriya .
Yace a lokacin da aka baiwa Najeriya ‘yancin kai Turawa na ganin itace giwar Africa kuma suna girmama ta amma daga baya wannan girman ya dusashe.
Obasanjo yayi kira ga matasa da su tashi tsaye su karbe mulki daga hannun tsaffin dake mulkar Najeriya a yanzu yace amma idan suka bari abubuwa suka ci gaba da faruwa a haka, babu inda kasar zata.