
Kakakin majalisar dattijai, Sanata Godswill Akpabio ya koka da irin halayyar Sanata Natasha Akpoti inda yace bai san wane irin tunani gareta ba.
Sanata Godswill Akpabio yace ta kawowa kwamitin da’a na majalisar dattijai korafi, ba’a gama bincike ba ta tafi ta kai kara kotu, can ma ba’a gama shari’a ba ta tafi ta kai korafi majalisar Dinkin Duniya.
Sanata Godswill Akpabio yace irin wannan abun ne zai iya sawa a daina baiwa mata mukaman siyasa.